<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>302</hymn_number>
<title>Ƙauna daga Allah Ce, Wannan Na Sakankance LW302</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ƙauna daga Allah ce, wannan na sakankance,
 Batun nan na Yesu ne, Allah ƙauna ne.

[V2]
 2) Ƙauna ba ta jin kishi, ba ta rashin hankali,
 Tana kuwa da haƙuri, Allah ƙauna ne.

[V3]
 3) Tana kuwa da nasiha, ƙauna ba ta kumbura,
 Ba ta kuwa jin cakuna, Allah ƙauna ne.

[V4]
 4) Ƙauna tana jurewa, ƙauna ba ta nukura,
 Haka cikin abu duka, Allah ƙauna ne.

[V5]
 5) Allahna, ƙaunatacce, kyautar ƙauna taka ce,
 Ba ta ƙarewa daɗai, Allah ƙauna ne.</lyrics>
</song>